Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarta cewa: Firaministan Spain Pedro Sanchez ya yi ishara da cewa: Yanzu aikinmu shi ne kokarin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da samar da zaman lafiya.
Zaman lafiya ba yana nufin mantawa ko gujewa hukunci ba, kuma a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da yunkurin matakai a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya.
Kamar yadda aka sani Taron sulhu na Sharm Sheikh a Masar, wanda aka kammala tare da rattaba hannu kan wata yarjejeniya tsakanin Amurka, Qatar, Masar da Turkiyya mai suna "Yarjejeniyar Gaza" ya janyo cece-ku-ce a shafukan sada zumunta. Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa "yakin ya kare", amma da yawa sun nuna shakku kan wannan ikirari.
Your Comment